Arsenal zata kara farashin tikitin shiga Emirates

arsenal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsenal

Arsenal zata kara farashin tikitin shiga kallon wasa a filin Emirates da kashi shida da rabi cikin dari a kakar wasa mai zuwa.

Tun shekara ta 2005 rabon da Gunners ta lashe gasa, amma ta ce karin farashin tikitin nada nasaba da hauhawar farashin kayayyaki a Birtaniya.

Sai dai kungiyar masu goyon bayan Arsenal wato Aisa ta nuna fushinta akan batun.

Kakakin Aisa din yace "mun ji takaicin wannan lamarin kuma hakan na nufin cewar wasu magoya baya ba zasu iya sayen tikiti ba anan gaba".

Shugaban Arsenal Ivan Gazidis ya jaddada cewar karin farashin tikitin shine na farko cikin kakar wasanni uku.

A watan Fabarairu, Arsenal ta tafka hasarar fan miliyon biyu da rabi a watanni shida na shekara ta 2010.

Kamar yadda adreshin intanet na Arsenal ya nuna cewar sabon farashin tikintin zai kai fan talatin da hudu zuwa casa'in da shida a kowane wasa.