Mourinho ya bata Real Madrid-Calderon

mourinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jose Mourinho yana kalabantar alkalin wasa

Tsohon shugaban Real Madrid Ramon Calderon ya ce hallayar Jose Mourinho ta bata kulob din lokacin wasan zagayen kusada karshe tsakaninta da Barcelona.

Real ta sha kashi a wajen babbar abokiyar hammayarta a gasar zakarun Turai a wannan makon, amma matsaloli ne ya dabaibaye fafatawar daga wajen 'yan kwallo da 'yan kallo da jami'an kulob din.

An kori Mourinho a bugun farko na wasan saboda ya nuna rashin amince akan baiwa dan wasanshi kati, sannan yayi kalaman da basu dace ba.

Calderon yace "yadda yayi magana ya janyowa Real Madrid matsala".

Har wa yau Calderon ya soki dabi'ar 'yan wasan Real saboda a cewarshi manyan kulob basa zargin alkalan wasa idan an doke su.