WAFU: Najeriya na kokari kare kofinta

siasia
Image caption Samson Siasia

Najeriya na kokarin kare kofinta na gasar cin kofin kasashen yammacin Afrika wato Wafu.

Tawagar 'yan wasan Super Eagles dake taka leda a cikin gida na rukuni guda ne da Nijer da Mali da kuma Liberia.

A shekarar data gabata, 'yan wasan karkashin jagorancin Daniel Amokachi sun lashe gasar ba tare da wata kasa ta samu galaba akansu ba, inda suka doke Senegal a wasan karshe.

A wannan karo Samson Siasia ne zai jagoranci tawagar Najeriya,abinda zai bashi damar lura da 'yan kwallon kasar dake cikin gida.

Bayan da kasar ta kasa tsallakewa zuwa gasar cin kofin Afrika na wasan dake taka leda a ciki gida wato CHAN, a yanzu Najeriya na son ta maidoda martabarta a idon sauran kasashen Afrika.

A rukuni na biyu kasashen Ghana da Senegal da Togo da kuma Gambia ne zasu kece raini.

Za a shafe kwanaki goma ana fafatawa a gasar a jihar Ogun a yayinda za a buga wasan karshe a ranar 15 ga watan Mayu.