Amos Adamu ya daukaka kara zuwa kotun wasanni

adamu
Image caption Amos Adamu

Tsohon jami'in hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa Amos Adamu ya kai kara kotun wasanni don kalubalantar dakatarwa ta shekaru uku da aka yi mashi daga shiga harkokin kwallon kafa bisa zargin kokarin karbar cin hanci.

Kotun ta ce Adamu ya bukaci an haramta dakatarwar da Fifa ta yi mashi.

Kwamitin da'a na Fifa ya kama Adamu da laifi a watan Nuwamban bara akan cewar ya nemi karbar cin hanci a kokarin kada kuri'a ga kasar da zata dauki bakuncin gasar cin kofin duniya a shekara ta 2018 da 2022.

An dakatar da shi sannan kuma ya rasa kujerarshi a kwamitin zartarwar Fifa.

Kotun sauraron kararrakin wasanni har ila yau ta ce Ahongalu Fusimalohi shima yana kalubalantar dakatarwar shekaru biyu da aka yi mashi a kotun.

Kawo yanzu dai kotun bata saka ranar fara sauraron karar ba.