Alessandro Del Piero ya sabunta kwangilarshi Juventus.

del piero
Image caption Alessandro Del Piero

Shahararen dan kwallon Italiya Alessandro Del Piero ya kara wa'adin kwangilarshi da shekara guda a Juventus.

Del Piero mai shekaru 36 ya kasance tare da Juve tun shekarar 1993, inda ya lashe gasar Serie A biyar da Copa Italiya daya da kuma na zakarun Turai a shekarar 1996.

Ya kuma lashe gasar 2005 dana 2006 tare da ita amma sai aka kwace bayan an kamasu da laifin magudi a wasa, sai suka koma gasar Serie B inda Juve ta lashe kofin tare da Del Piero a shekara ta 2007.

Del Piero yace"Ina jin dadin kaina anan, kuma zan cigaba har zuwa badi".

Ya bugawa Italiya wasanni 91 inda ya zira kwallaye 27 kuma yana cikin tawagar data lashe gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006.