Fifa zata sassauta doka akan 'yan kwallo

fifa
Image caption Kofin da ake fafatawa akai a gasar kwallon duniya

Fifa na tunanin sassauci akan dokarta data shafi sauya kasar da 'yan kwallo zasu takawa leda a lokacin taronta na koli.

Taron kolin kuma zai nemi baiwa kwamitin gudanarwa karfin dakatar da wakilan kasashe a Fifa.

Amma babban ajandar taron na ranar daya ga watan Yuni shine zaben shugaban kungiyar tsakanin Sepp Blatter da kuma Mohamed Bin Hammam.

Fifa kuma zata tattauna akan shawarar cewa duk dan kwallon da ya wuce shekaru 18 zai iya canza kasar da zai bugawa kwallo idan ya shafe shekaru uku a cikin wannan kasar sabanin shekaru biyar da ake amfani dashi a yanzu.

Blatter ya nuna fargabar cewa idan aka yi haka tabbas za a samu 'yan Brazil da dama suna bugawa wasu kasashen a lokacin gasar cin kofin duniya.

Taron kuma zai bukaci amincewa da sabuwar doka wacce Fifa zata iya amfani da ita wajen sauya alkalin wasa idan har aka gano cewar bai dace da ya jagoranci fafatawa ba.