Mancini na fargaba akan lafiyar Tevez

tevez Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Carlos Tevez da kocinsa Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce Carlos Tevez ba zai buga wasan karshe na gasar cin kofin FA ba a ranar 14 ga wata idan har bai murmure ba don karawa da Tottenham a ranar Talata mai zuwa.

Tevez na fama da rauni a kafadarshi tun a watan Afrilu kuma bai buga wasan FA tsakaninsu da Manchester United ba.

Mancini yace "da kamar wuya ya buga wasanmu da Everton na ranar Asabar".

City dai zata fuskanci Stoke City a filin Wembley a wasan karshen na kofin FA, wanda shine na farko tuna shekarar 1981 da kungiyar ta buga.

Mancini kuma ya yi karin haske akan zawarcin da Bayern Munich ke yiwa dan kwallonshi Jerome Boateng, inda yace abune me kyau.

Mancini yace"nayi murna Bayern na son dan kwallo na, don hakan ya nuna cewar muna da manyan 'yan wasa".