Akwai wuya mu tsallake zakarun Turai-Redknapp

rednapp
Image caption Harry Redknapp

Kocin Tottenham Harry Redknapp ya amince da kamar wuya kungiyarshi ta samu gurbin zuwa gasar zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa bayan sun tashi kunen doki tsakaninsu da Blackpool a ranar Asabar.

Bayan ta buga wasanni hudu ba tare da nasara ba, a yanzu Spurs nabin bayan Manchester City da maki shida a yayinda ya rage wasanni uku a kamalla gasar.

Redknapp wanda babban dan wasanshi Gareth Bale ke jinya ya ce "abin zai bamu wuya matuka".

Ya kara da cewar nasararsu ta tsallakewa zuwa zagayen gabda na kusada karshe a gasar zakarun Turai abune da suka sa rai.

Akan batun raunin Bale kuwa, Redknapp yace za a dauki hoton idon sawun dan kwallon a ranar Litinin.