Makomata na hannun Chelsea - Ancelotti

Carlo Ancelotti
Image caption Carlo Ancelotti yana cikin rashin tabbas game da makomarsa

Kocin Chelsea Carlo Ancelotti na fatan kammala kwantiraginsa a Chelsea, sai dai ya amince cewa lamarin ba a hannunsa ya ke ba.

Ancelotti ya jagoranci Chelsea ta lashe gasar Premier da FA a bara.

Sai dai, kocin dan kasar Italiya na shirin kammala kakar bana ba tare da ya lashe kofi ba, bayan da Manchester United ta doke su da ci 2-1 ranar Lahadi.

"Saura shekara guda kwantiragi na ta kare kuma zanso na kammala, amma wannan lamari na hannun kulob din," a cewarsa. "Muna da sauran wasanni biyu, za mu jira mu gani."

Chelsea sun garzaya Old Trafford ne domin neman nasarar da za ta basu damar kamo Manchester United.

Amma kwallayen da Javier Hernandez da Nemanja Vidic suka zira sun kusan tabbatarwa da United gasar League ta 19 a tarihi.