Bale ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana

bale Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gareth Bale da Harry Redknapp

Tottenham ta tabbatarda cewa Gareth Bale ba zai kara taka leda ba a kakar wasa ta bana saboda rauni a idon sawunshi.

Amma dai kungiyar ta ce ana saran zai murmure kafin a fara kakar wasa mai zuwa.

Bale ya jimu ne a lokacin wasansu da Blackpool a karshen mako inda aka tashi kunen doki.

Kocin Spurs Harry Redknapp ya ce Bale yayi ta fama da rauni daban daban a kakar wasa abinda ya haddasi bai taka rawar daya saba ba a bana.

Sanarwar da kulob din ta fitar ta ce "Gareth zai shafe kwanaki goma sha biyu sanye da takalmi na gyaran rauni a kafarshi.

Wannan raunin da dan Wales mai shekaru 21 ya samu ya tilastashi fasa shiga gasar kasashe hudu da za a fara a wannan watan inda Wales zata buga.