Kocin Liverpool ya yabawa 'yan wasanshi

Kenny Dalglish Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption A watan Janairu ne Kenny Dalglish ya koma Liverpool

Kocin Liverpool Kenny Dalglish ya yabawa 'yan wasanshi a daidai lokacin da suke ci gaba da haskakawa inda suke lallasa Fulham da ci 5-2.

Dalglish ya sauya yadda Liverpool ke taka leda inda daga tsakiyar tebur suka hawo sama inda suke gab da buga gasar Europa.

"Abin mamaki ne. Babu wanda ya zaci yaran za su haskaka kamar haka tun watan Janairu," a cewarsa. "Koda ba mu samu mataki na biyarba, to hakika sun yi kokari."

Dalglish ya maye gurbin Roy Hodgson a watan January, lokacin da Liverpool ke cikin tsaka mai wuya a mataki na 12 a tebur.