Faransa ta wanke Blanc akan wariyar launin fata

blanc
Image caption Laurent Blanc

Ministan wasannin Faransa ta wanke kocin 'yan kwallon kasar Laurent Blanc daga aikata laifin daya shafi wariyar launin fata.

Chantal Jouanno ta ce babu hujjar akan cewar Blanc ya karya doka ta hanyar tattauna batun kayyade bakake da larabawan da zasu wakilin tawagar matasan Faransa.

Blanc ya ce an yiwa kalamanshi mummunar fassara.

Shi da wasu ne suka tattauna yadda za a hana matasan 'yan kwallon da Faransa ta horar daga bisani kuma su bugawa wata kasar.

Ms Jouanno ta ce hukumar kwallon Faransa ce keda alhaki akan makomar darektan kwallo Francois Blaquart wanda aka dakatar.

Wannan lamarin ya jefa kwallon Faransa cikin rudu kasada shekara guda da aka nada Laurent Blanc a matsayin koci bayan taka mummunar rawar da kasar ta yi a gasar kwallon duniya a Afrika ta Kudu a bara.