Jami'an Fifa hudu sun nemi cin hanci-Triesman

triesman
Image caption Lord Triesman

Tsohon shugaban hukumar kwallon Ingila Lord Triesman yayi zargin cewar jami'an Fifa hudu sun nemi cin hanci don su baiwa Ingila kuri'ar damar daukar bakuncin gasar cin kofin duniya a 2018.

Triesman wanda da farko shine shugaban kwamitin tabbatar da Ingila ta samu damar, ya yi zarginne akan Jack Warner da Nicolas Leoz da Ricardo Teixeira da kuma Worawi Makudi.

A cewarshi dabi'arsu bai "dace da tsari na aiki ba".

Triesman ya shaidawa kwamitin al'adu da wasanni na majalisar wakilan Birtaniya cewar zai gabatarwa da hukumar kwallon duniya Fifa hujjarshi.

Ya kara da cewar hukumar FA da farko taki kai kara ne don kada hakan ya janyowa Ingila kafar angulu.

Shugaban kwamitin na majalisar wakilan John Whittingdale ya ce zasu rubutawa shugaban Fifa Sepp Blatter ya gudanar da bincike akan hujjar ba tare da bata lokaci ba.