Za mu lashe Premier a wasan Blackburn - Vidic

Nemanja Vidic Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Nemanja Vidic yana tattaunawa da alkalin wasa

Kyaftin din Manchester United Nemanja Vidic ya nemi takwarorinsa da su dage su doke Blackburn Rovers domin su lashe gasar League a karo na 19.

Vidic ya shaida wa jaridar Daily Mail ta Burtaniya cewa, yana da mahimmanci idan United ta lashe gasar a wasan Blackburn Rovers a karshen mako.

"Mun ba da tazarar maki shida kuma saura wasanni biyu. Don haka za mu maida hankali a kan wasanmu da Blackburn. Ba ma so mu kai wasan karshe kada mu shiga cikin damuwa.

Manchester United ta doke Chelsea 2-1 a ranar Lahadi inda ta baiwa Chelsea tazarar maki shida kuma saura wasanni biyu a kammala gasar.

A yanzu suna bukatar su yi canjaras ne kawai a daya daga cikin wasanni biyun da ya rage musu domin su lashe gasar a karo na 19. Dan wasan ya kuma jinjinawa koci Alex Ferguson, a kan yadda yake jagorantar kungiyar ga irin nasarorin da take samu.