Mun shiryawa gasar zakarun Turai - Mancini

Roberto Mancini Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Roberto Mancini ya fuskanci kalubale da dama a kakar bana

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya yi alkawarin taka rawar gani a gasar zakarun Turai bayan da kulob din ya doke Tottenham 1-0 domin kaiwa gasar a karon farko a tarihi.

City ta doke Tottenham da ci daya mai ban haushi a ranar Talata inda ta tabbatar da matsayinta na hudu a kan teburin gasar Premier.

"Lokacin da na zo, na fada cewa cikin shekaru biyu ko uku City za ta zamo daya daga cikin manyan kungiyoyin kwallon kafa a Turai".

"Amma na yi farin ciki ga kungiyar da kuma magoya bayan ta."

Nasarar ta City ta zo ne bayan da dan wasan Tottenham Peter Crouch, ya zira kwallo a ragarsu - Crouch din ne dai ya zira kwallon da ta baiwa Tottenham damar zuwa gasar Turai a bara.