'Watakila Ingila ta fice daga Fifa'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Lord Triesman, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na Ingila.

Ministan wasanni a Ingila Hugh Robertson ya ce watakila Ingila ta fice daga hukumar kwallon kafa ta Ingila wato Fifa, muddin bata magance matsalar cin hanci da rashawa ba a hukumar.

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa na Ingila Lord Triesman ya zargi wasu jami'an Fifa hudu da neman cin hanci domin nuna goyon bayan ga kokarin Ingila na karbar bakoncin gasar cin kofin kwallon kafa na duniya a shekarar 2018.

"Akwai wani yinkuri na gyara da kuma daidaita al'amura a hukumar FIFA ta cikin gida." In ji Robertson.

"Amma idan Fifa ta gaggara yin gyara, zamu iya ficewa daga hukumar."

Triesman wanda da farko shine shugaban kwamitin tabbatar da Ingila ta samu damar, ya yi zarginne akan Jack Warner da Nicolas Leoz da Ricardo Teixeira da kuma Worawi Makudi.

A cewar shi dabi'arsu bai "dace da tsari na aiki ba".

Lord Triesman ya shaidawa kwamitin al'adu da wasanni na majalisar wakilan Birtaniya cewar zai gabatarwa da hukumar kwallon duniya Fifa hujjarshi.

Ya kara da cewar hukumar FA da farko taki kai kara ne don kada hakan ya janyowa Ingila kafar angulu.

Shugaban kwamitin na majalisar wakilan John Whittingdale ya ce zasu rubutawa shugaban Fifa Sepp Blatter ya gudanar da bincike akan hujjar ba tare da bata lokaci ba.