Hayatou ya musanta zargin cin hanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Issa Hayatou

Shugaban Hukumar kwallon Afrika Caf, Issa Hayatou ya musanta zargin cin hanci da ake mishi na kada kuri'ar daukar bakonci gasar cin kofin duniya.

An dai zargi jami'in ne da karban cin hanci a wani bincike da majalisar dokokin burtaniya ta gudanar domin gano dalilan da yasa ba'a baiwa Ingila damar daukar bakoncin gasar cin kofin duniya ba na shekarar 2018.

An dai zargi Issa Hayatou da shugaban hukumar kwallon kafa na Ivory Coast Jacques Anouma, da karbar dala miliyan daya da rabi domin baiwa Qatar damar daukar bakocin gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.

An bayanan da aka wallafa a shafin Caf, Hayatou ya bayyana zargin cin hanci a matsayin kazafi.

A baya ma an zargi Hayatou da karbar kudi domin kadawa kasar Morocco kuri'a a matsayin wadda zata dauki bakonci gasar cin kofin duniya ta shekarar 2010.