Jacques Anouma ya musanta zargin cin hanci

Shugaban hukumar kwallon Ivory Coast Jacques Anouma ya bi sahun shugaban Caf Issa Hayatou inda ya musanta zargin neman cin hanci domin siyarda kuri'u.

An zargi jami'an Fifa biyu ne da siyarda kuri'un su, idan suka zabi Qatar a matsayin kasar da za ta dauki bakonci gasar cin kofin duniya a shekarar 2022.

An dai zargi jami'an ne a wani bincike da majalisar dokokin Burtaniya ta gudanar bincike domin dalilan daya sa Ingila bata samu damar daukar bakoncin gasar cin kofin duniya ba na shekarar 2018.

Anouma ya ce zargin bata suna ne kawai.

"Ganin irin nauyin laifi da ake zargi na da shi, ina marhabin da binciken da Fifa za ta gudanar da domin a tantance gaskiyan al'amarin."