Barcelona ta lashe gasar laliga ta Spaniya

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Barcelona ta lashe gasar a karo na uku a jere bayan ta buga kunnen doki da Levante inda su ka tashi daya da daya.

Barca dai ta lashe gasar ne, inda ta fi kungiyar madrid da maki shida, yayinda kuma ya rage masu wasanni biyu a gasar.

A karawa biyu da suka yi, Barca ce tayi galaba a wasan farko sannan kuma suka buga kunnen doki a wasa na biyu.

A wasan da Barca ta buga da Levante, Seydou Keita ne ya zura kwallon farko kafin Felipe Caicedo ya fanshewa Levante.