Dalglish ya rataba hannu a kwantaragi da Liverpool

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Kocin Liverpool, Kenny Dalglish

Kenny Dalglish ya rataba hannu a kwantaragi na tsawon shekaru uku domin jogorantar kungiyar Liverpool.

Kocin wanda dan asalin Scotland ne ya karbi aiki ne daga Roy Hodgson na wucin gadi a watan Junairun data gabata.

"Ina matukar farin ciki da wannan damar da aka bani." In ji Dalgish

"Da nazo a watan Junairu, babu alkawarin da nayi, naga wata damace da zai taimaka in nuna kwarewa ta a harkar tamoula."

Kocin ya dawo kungiyar ne a karo na biyu, inda ya taka leda a shekaru 1970's da kuma 80's.

Dalglish ya taimakawa Liverpool matuka bayan zuwansa kungiyar, inda a yanzu haka take ta hudu a kan tebur.