Ajax ta lashe gasar kwallon Holland

ajx Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Ajax ta lashe gasar a karon farko tun shekara ta 2004

Ajax ta lashe gasar kasar Holland karo na talatin bayan ta doke FC Twente daci uku da daya a filin Amsterdam Arena.

Twente a makon daya gabata ta samu galaba akan Ajax daci uku da biyu a gasar cin kofin kasar Holland.

Siem de Jong ne ya ciwa Ajax kwallayenta biyu a yayinfa Denny Landzaat ya zira kwallo daya a ragarsu ta Twente bisa kuskure.

Wannan ne karon farko tun shekara ta 2004 da Ajax ta kashe gasar Holland.

Haka zalika wannan ne kofin farko da Frank de Boer ya lashe tare da Ajax tunda ya maye gurbin Martin Jol a Disamba.