Birnin Manchester na cike da bukukuwa

city Hakkin mallakar hoto a
Image caption 'Yan Man City suna murna

Birnin Manchester ya kammala nasarar cin kofina biyu a ranar Asabar a yayinda biyu daga cikin kungiyoyin kwallon kafa na yankin suka lashe gasar premier dana FA.

Manchester United ta tashi kunen doki ne tsakaninta da Blackburn don lashe gasar premier sau goma sha tara a yayinda ita kuma Machester City ta lashe kofin FA bayan ta doke Stoke daci daya a filin Wembley.

Wayne Rooney ne yaciwa United kwallon daya tabbatar mata da kofin sai kuma Yaya Toure ya zira kwallon dayan daya baiwa City damar lashe kofi a karon farko cikin shekaru talatin da biyar.

Tunda farko a wannan makon tawagar 'yan kwallon Roberto Mancini sun doke Tottenham daci daya me ban haushi nasarar data tabbatarwa da City gurbin zuwa gasar zakarun Turai a karon farko.

Toure yace"abin murna ne mun lashe kofi kuma zamu buga gasar zakarun Turai".

A ranar 22 ga wannan watan ne za a baiwa United kofin data lashe bayan wasanta da Blackpool.