Uefa ta wanke Busquets bisa zargin da Real tayi

 Busquets Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Busquets da Marcelo lokacin karawar

Dan wasan Barcelona Sergio Busquets zai buga wasan karshe na gasar zakarun Turai tsakaninsu da Manchester United bayan an wanke shi da zargin kalaman wariyar launin fata.

Uefa tayi watsi da zargin da Real Madrid tayi akan Busquets na cewar yayi wa dan Brazil Marcelo kalaman batanci.

Sanarwar da Barcelona ta fitar a shafinta na Intanet ta ce "Uefa taki amincewa da zargin da Real Madrid ta gabatar".

Barcelona zata kece raini da Manchester United a wasan karshen a filin Wembley a ranar Asabar 28 ga watan Mayu.

Real Madrid ta yi zargin cewar Busquets ya kira Marcelo a matsayin biri a wasan da Barca ta doke Real daci biyu da nema.