Caf na goyon bayan Blatter akan Hammam

baltter
Image caption Sepp Blatter da Mohammed Bin Hammam

Hukumar dake kula da kwallon Afrika wato Caf ta bayyana goyon bayanta akan shugaban Fifa Sepp Blatter don ya cigaba da jan ragamar kwallo a duniya.

Blatter na fuskantar kalu bale ne daga wajen shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya Mohamed Bin Hammam a zaben da za ayi a wata mai zuwa.

Akwai dai wakilan Caf 53 da zasu kada kuri'a lokacin zaben.

Blatter ya samu goyon bayan Caf ne a taron da akayi a birnin Alkahira a ranar Litinin.

Yankin Oceania da Turai da kuma kudancin Amurka dai a baya duk sun nuna goyon bayansu na Blatter ya zarce a karo na hudu akan kujerar Fifa.

Wakilan Fifa 208 zasu kada kuri'a a ranar don zabe tsakanin manyan giwayen biyu.