Maradona ya zama kocin Al Wasl a Dubai

maradona
Image caption Diego Maradona

Diego Maradona ya kulla yarjejeniya ta shekaru biyu a matsayin kocin kungiyar Al Wasl ta Dubai.

Kungiyar a wata sanarwa ta ce"zan tabbatar muku da cewar mun dauki hayar daya daga cikin gawurtattun 'yan kwallo a duniya".

An kulla yarjejeniyarce bayan sasantawa mai tsawo da Maradona mai shekaru hamsin.

A cewar kulob din yana fatar Maradona zai ciyar dasu gaba.

Shugaban Al Wasl Marwan Bin Bayat yace kwangilar tayi daidai da martabar gawurtaccen dan kwallon.