Ghana ta gayyaci Essien don karawa da Congo

essien
Image caption Micheal Essien

Ghana ta gayyaci dan wasan Chelsea Micheal Essien cikin tawagarta bayan ya shafe watanni goma sha shida yana hutu.

An saka Essien cikin 'yan wasa 24 da kocin Ghana Goran Stevanovic ya gayyata don buga wasan share fage na neman cancantar buga gasar kwallon Afrika tsakaninsu da Congo sai kuma wasan sada zumunci da Koriya ta Kudu.

Dan wasan mai shekaru 28 ya dakatar da bugawa Ghana kwallo ne saboda rauni.

Har wa yau Kevin Prince Boateng da Opoku Agyemang suma an gayyacesu bayan hutun da suka dauka don murmurewa daga rauni.

Black Stars zata kara da Congo a ranar hudu ga watan Yuni sai kuma ta hadu da Koriya ta Kudu a ranar bakwai ga wata.