Mancini ya samu garabasar fan miliyon guda

mancini Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Roberto Mancini

Za a baiwa kocin Manchester City Roberto Mancini garabasar fan miliyon guda saboda jagorantar kulob din zuwa gasar zakarun Turai.

Wannan ne karon farko da City ta samu gurbin zuwa gasar zakarun Turai kuma akwai yiwuwar yaran Mancini din su iya zama na uku akan tebur idan suka doke Stoke City.

Sheikh Mansour wanda ke mallakar kulob din ya bada umurnin cewar kasancewa cikin kulob hudu na farko a gasar premier shine abinda suka sa a gaba inda ya kashe fiye da fan miliyon 350 tun daga siyen kulob din a watan Agustan shekara ta 2009.

Kulob din yayi alkawarin baiwa Mancini garabasar fan miliyon guda akan albashinsa na fan miliyon uku a kowanne shekara idan har ya kaisu gasar zakarun Turai.

Har wa yau akwai garabasa na jiran Mancini saboda jagorantar kulob din ya lashe kofin farko cikin shekaru 35.

Mancini mai shekaru 46 ya koma Manchester City ne a watan Disamban 2009 bayan korar Mark Hughes.