Inzaghi ya sabunta kwangilarshi a AC Milan

Filippo Inzaghi Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Filippo Inzaghi

Shahararren dan kwallon Italiya Filippo Inzaghi ya sabunta yarjejeniyarshi da AC Milan na karin shekara guda.

Amma dai Andrea Pirlo ya ce yanason barin kungiyar bayan ya shafe shekaru goma tare da ita. Pirlo mai shekaru 32 ya koma Milan ne a shekara ta 2001 daga babbar abokiyar hammayarta Inter Milan.

Ya soma kwallonshi ne a Brescia kafin ya koma Inter a shekarar 1998 amma an taba bada aronshi a Reggina.

Pirlo ya lashe gasar zakarun Turai biyu dana Serie A biyu tare da Milan sai kuma gasar cin kofin duniya tare da Italiya a shekara ta 2006.

Anashi bangaren dai Filippo Inzaghi ya shafe kakar wasa ta bana yana jinyar rauni a idon sawunshi.

Dan shekaru 37, ya koma AC Milan ne daga Juventus a shekara ta 2001 bayan ya taka leda a Parma da Atalanta da Verona da kuma Leffe.

Inzaghi shima ya lashe kofin duniyada Italiya kuma ya lashe gasa a Milan kamar Pirlo sai dai shi ya taba lashe kofi da Juventus.