Tavez na son zama a City - Mancini

Carlos Tevez Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Carlos Tevez ya taka rawa sosai a Ciity a kakar bana

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya ce kyaftin din kulob din Carlos Tevez na son ci gaba da zama a kungiyar bayan da suka lallasa Stoke da ci 3-0.

Makomar dan wasan na Argentina ta shiga cikin rudu tun bayan da ya mika bukatar izinin tafiya a watan Janairu.

"Yana da kwantiragin shekara biyar kuma ya gaya mana cewa yana so ya ci gaba da zama," a cewar Mancini bayan da Tavez ya zira kwallaye biyu abinda ya taimakawa City ta koma mataki na uku a tebur.

Kocin ya kara da cewa: "Ya fada a baya. Bai taba samun wata matsala da mu ba."

Kalaman na Mancinin sun yi kama da wadanda suke fitowa daga bakin Tavez da kansa.

Jim kadan bayan nasarar da suka samu a kan Stoke a wasan karshe na gasar cin kofin FA.

Tavez ya bayyana cewa: "Akwai batun da ya kamata mu shawo kai - kuma shi ne na nisan da ke tsakani na da iyalina."