An sabunta: 18 ga Mayu, 2011 - An wallafa a 16:37 GMT

Kamaru ta gayyaci Song cikin tawagarta

Alex Song

Alex Song

Kamaru ta gayyaci dan wasan Arsenal Alex Song cikin tawagarta a karon farko tun bayan gasar cin kofin kwallon duniya da akayi a bara.

Dan wasan na daga cikin tawagar 'yan kwallon 23 da kocin Indomitable Lion Javier Clemente ya gayyata don fuskantar Senegal a wasan share fagen neman gurbin zuwa gasar kwallon kasashen Afrika a badi.

A halin yanzu dai Kamaru na cikin halin kila wa kala a kokarinta na zuwa gasar cin kofin Afrika da za ayi a Gabon da Equitorial Guinea a yayinda rage wasanni uku a kamalla wasanni share fagen.

Sakatare Janar na hukumar kwallon Kamaru Fecafoot Tombi Aroko ya ce yana fatar gayyatar sabbin jini a cikin tawagar zai taimaka su ciyar da kwallon Kamaru gaba.

Tawagar: Guy Roland Ndy Assembe (Nantes, France), Idriss Carlos Kameni (Espanyol, Spain), Charles Itandje (Atromitos FC, Greece), Sebastien Bassong (Tottenham Hotspur, England), Benoit Angbwa (FC Anji Makhatch, Russia), Patrick Abouna Ndzana (Les Astres FC, Cameroon), Nicolas Nkoulou (Monaco, France), Gaetan Bong (Valenciennes, France), Henri Bedimo (RC Lens, France), Stephane Mbia (Olympique Marseille, France), Matthew Mbuta (Crystal Palace Baltimore, USA), Eyong Enoh (Ajax Amsterdam, Holland), Alex Song (Arsenal, England), Landry Nguemo (AS Nancy, France), Andre Ndame Ndame (Coton Sport), Aurelien Chedjou (Lille, France), Benjamin Moukandjo (Monaco, France), Eric Choupo-Moting (Hamburg, Germany), Achille Webo (Mallorca, Spain), Samuel Eto'o (Inter Milan, Italy), Vincent Aboubakar (Valenciennes, France), Benoit Assou-Ekotto(Tottenham Hotspur, England), Ngako Deutcha Duvalois (Sable Bati)

BBC navigation

BBC © 2014 BBC ba ta da alhakin abubuwan da ke kunshe a shafukan da ba nata ba.

Wannan shafin zai fi kyan gani, idan an shige shi da browser mai salo na bai daya. Yayinda za ka iya samun damar duba abin da wannan shafin ya kunsa a browser da kake da ita a halin yanzu, ba za ka samu damar ganin dukkan abin da shafin ya kunsa kamar yadda ya kamata ba. Dubi yiwuwar inganta manhajar browsar ka, ko kuma ka samu browser mai salo na bai daya, idan har za ka iya.