Ana zargin Armstrong da shan haramtattun kwayoyi

Image caption Lance Armstrong

Wani abokin wasan tuka keke zakaran gasar tseren keke wato Lance Armstrong ya zargi dan tseren da shan haramtatcen kwaya ta EPO.

Tyler Hamilton ya zargi Armstrong wanda ya lashe gasar Tour de France sau hudu da shan kwayar EPO a gasar da aka shirya a shekarar 1999.

Armstrong, wanda ya dade yana karyata zargin ya ce; " Ba'a ta samu na da laifi ba bayan gwaji."

Hamilton, mai shekarun haihuwa 40, na taba fuskantar dakatarwa na shekaru biyu daga 2005-2007 bayan an same shi da laifin haramtattun kwayoyi.

"Na ga EPO a firjin sa, kuma na ga yana yiwa kansa allura fiye da so daya." In ji Hamilton.