Juventus ta kori kocin 'yan kwallonta

Del Neri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luigi Del Neri

Juventus ta sallami kocin 'yan kwallonta Luigi Del Neri amma zai jagoranci tawagar a wasanta na karshe a ranar Lahadi.

Del Neri ya shaidawa manema labari"kulob din sun gaya mani matakin da suka dauka a cikin wannan makon"

Juventus ta buga kakar wasanni biyu kenan a jere babu taka rawar gani, kuma a halin yanzu itace ta bakwai akan teburin Serie A.

Tsohon dan wasan Juve Antonio Conte mai shekaru 41 wanda ya kai Siena zuwa gasar Serie A, shine ake tunanin zai maye gurbinshi.

Del Neri, mai shekaru 60 ya koma Juventus ne a watan Mayun 2010 bayan ya jagoranci Sampdoria ta samu gurbin zuwa gasar zakarun Turai.

A baya ya jagoranci kungiyoyin Atalanta da AS Roma da kuma FC Porto.