Ronaldo ya kafa sabon tarihi a La Liga

ronaldo Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gawurtattacen dan kwallo Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya kafa sabon tarihi na zira kwallo arba'in a kakar wasa guda a gasar La Liga bayan ya ci kwallaye biyu a wasan da suka doke Almeria.

Ya zira kwallon farko a minti hudu da farawa sai kuma na biyu a minti na 77, a yayinda Real ta lallasa Almeria daci takwas da daya.

Kwallaye biyun daya zira sun sashi gaban dan wasan Real Hugo Sanchez da kuma na Athletic Bilbao Telmo Zarra wadanda a baya sune ke rike da tarihin cin kwallaye mafi yawa a La Liga.

Sanchez ya zira kwallaye 38 a kakar wasa na 1989/90 shima Zarra yaci kwallaye 38 a 1959/60.

A lokacin wasan Emmanuel Adebayor yayi bankwana da cin kwallaye uku a Real Madrid saboda kwangilarshi ta aro daga Manchester City ta kare.

Ronaldo yaci kwallaye tara a wasanni uku daya bugawa Real inda ya zira kwallaye 53 a kakar wasa ta bana.

Ronaldo yace"cin kwallaye dayawa nada wuya, amma ina godiya ga abokan wasa na".

Ronaldo da dan wasan Barcelona Lionel Messi sun kasance 'yan wasan gasar Spain na farko da suka zira akalla kwallaye 50 a kakar wasa daya.

Messi bai buga wasan da Barcelona ta casa Malaga daci uku da daya a ranar Asabar.

Amma dai dan Argetina din nada damar kara kwallo akan 52 daya ci kawo yanzu, saboda yana da wasan zakarun Turai tsakaninsu da Manchester United a ranar Asabar.