Ya kamata a cigaba da kashe kudi-Mancini

mancini Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Roberto Mancini

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya hakikance akan cewar dole ne masu kulob din su cigaba da kashe kudi, idan har suna son a kara karfin tawagar don fafatawa a kakar wasa mai zuwa.

City ta kamalla kakar wasa ta bana cikin anashawa bayan lashe gasar kofin FA da kuma samun gurbin zuwa gasar zakarun Turai da kuma kasancewa na uku akan tebur.

Sai dai shugaban kulob din Khaldoon Al-Mubarak wanda suka kashe fiye da fan miliyan dari hudu tun sayen kulob din a shekara ta 2008, ya bayyana cewar a wannan karon zasu yi taka-tsantsan wajen cefano 'yan wasa.

Mancini yace"muna son sayen karin 'yan kwallo don inganta tawagarmu".

Ya kara da cewar"zaka iya kashe kudaden masu yawa amma babu tabbas akan nasara, sai dai idan baka kashe kudi ba, ba zaka samu nasara ba".