2022:Qatar ta musanta zargin bada cin hanci

qatar Hakkin mallakar hoto None
Image caption Qatar 2022

Jami'an shirya gasar cin kofin duniya a Qatar a shekara ta 2022 sun bayyana zargin bada cin hanci don a zabe kasar a matsayin"abin damuwa, raini kuma zuki ta mallo".

A ranar 10 ga watan Mayu, 'yan majalisar dokokin Birtaniya sun buga hujja a jaridar Sunday Times akan cewar Qatar ta biya jami'an Fifa biyu daga Afrika dala miliyan daya da rabi kowanne.

Qatar a sanarwar data fitar ta amince a bincike akan hujjar kamar yadda Fifa keyi a halin yanzu.

Jami'an Qatar sun soki jaridar Sunday Times akan zargin baiwa Issa Hayatou da Jacques Anouma cin hanci.

Shugaban Fifa Sepp Blatter yaki amincewa da batun sake takara akan zaben na 2022 idan har ya tabbata cewar zargin gaskiya ne.

Blatter na takara ne da dan Qatar Mohammed Bin Hammam a zaben shugaban Fifa a ranar daya ga watan Yuni.