Vettel ya lashe gasar tseren motoci ta Spain

Sebastian Vettel Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Zakaran gasar tseren motoci na duniya Sebastian Vettel

Dan wasan Red Bull Sebastian Vettel ya doke takwaransa na McLaren Lewis Hamilton, inda ya lashe gasar tseren motoci ta Spanish Grand Prix.

Wannan ne karo na hudu da Vettel ya lashe gasar daga cikin biyar da aka fafata, amma Hamilton ya taka rawa a wasan share fage.

Takwaran Hamilton Jenson Button ya taka rawa inda ya kare a mataki na uku.

Dan wasan Ferrari Fernando Alonso ya kare a mataki na biyar bayan dan wasan Red Bull Mark Webber.

Sebastian Vettel wanda shi ne zakaran tseren na duniya ya bayyana cewa ya sha wuya matuka a gasar ta Spain, inda ya samu kansa da kyar.