Sergio Aguero son barin Atletico Madrid

aguero
Image caption Sergio Aguero

Dan kwallon Atletico Madrid Sergio Aguero ya sanarda kungiyar cewar yanason barinta.

Dan wasan Argentina mai shekaru 22 ya sabunta yarjejeniyarshi zuwa shekara ta 2014 a watan Junairu amma a yanzu ya canza ra'ayinshi na cigaba da zama a kungiyar.

Aguero yace"bayan shafe shekaru biyar, a yanzu inason in sauya sheka"

Chelsea, Liverpool, Manchester City da Tottenham duk suna zawarcin Aguero.

Ya kara da cewar"lokaci yayi da zan fadawa duniya cewar inason tafiya".

Aguero ya zira kwallaye 100 tun zuwanshi Atletico daga Independiente a shekara ta 2006.