Beckham ya jinjinawa Manchester United

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption David Beckham na taka leda ne a kungiyar LA galaxy

David Beckham ya ce lashe gasar Premier da Manchester United ta yi a bana shine mafi kayatarwa a tarihi.

Kocin Manchester, Manager Sir Alex Ferguson zai iya lashe gasar zakarun Turai a karo na uku, idan har kungiyar tayi galaba akan Barcelona a ranar asabar.

Tsohon dan wasan United, Beckham ya shaidawa BBC cewa, tawagar da kungiyar take da shi a yanzu tafi taka rawar gani a tarihi, kuma kofunan da suka lashe ya nuna hakan.

"Mutane sun soki 'yan wasan, amma sun taka rawar gani." In ji Beckham.

United dai ta kammala wasan ta a kakar wasan bana a gasar Premier da nasara a kan kungiyar Blackpool da ci hudu da biyu a yayinda ba'a doke kungiyar ba a kakar wasan bana.