Vuvuzela na iya yada cutar masassara

vuvuzela
Image caption Vuvuzela

Kakakin Vuvuzelas da 'yan kallo suka yi amfani dashi wajen murna a gasar cin kofin duniya a bara zai iya yada cuta, bayaga hayaniyar algaitar, kamar yadda kwararrun suka bayanna.

Busa Vuvuzelar dai sai an dage ake yi kamar yadda binciken PLoS One journal ya nuna.

Inda akwai cikowar mutane, mutum daya idan ya busa Vuvuzela zai iya yada cututukar dake yaduwa ta iska kamar masassara da tarin fika.

A halin yanzu dai masu shirya gasar Olympics na London a shekara ta 2012 na kokwanton barin ayi amfani da Vuvuzela ko kuma a'a.

Masu sukar algaitar na abin nada hadari saboda zai iya samarda karar data yi ta jirgin dake tashi sama.