Sakaci ne zai hana Barcelona doke United-Lineker

lineker Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Gary Lineker

Gary Lineker yace Manchester United zata lashe gasar zakarun Turai a ranar Asabar ne, idan har Barcelona ta buga banzan wasa.

Barca ta casa United a wasan karshe na shekara ta 2009 final kuma a yanzu ana ganin kamar itace zata samu nasara.

Tsohon kyaftin din Ingila Lineker yace "Idan Barcelona tayi wasa me kyau zata samu nasara".

Ya kara da cewar"Barca sai ta buga wasa mara kyau kafin United ta samu galaba ko kuma United idan ta taki sa'a".

A cewar Lineker duk da wasan a Ingila za a buga amma dai Barcelona tafi alamun nasara a wasan.

A makwan daya wuce ne dai kungiyoyin biyu suka lashe kofin gasar kasashensu na cikin gida.