West Brom da Odemwingie na tattaunawa akan kwangila

odemwingie
Image caption Osaze Peter Odemwingie

Kungiyar West Brom ta bude tattaunawa da Osaze Peter Odemwingie akan sabuwar yarjejeniya dashi, kamar yadda wakilin dan kwallon ya bayyana.

Dan Najeriya mai shekaru 29 shine yafi kowa zira kwallo a kulob din inda yaci kwallaye 15 a kakar wasanshi ta farko a gasar Premier ta Ingila.

Odemwingie ya taka rawar gani matuka wajen nasarar da kulob din ya samu inda ya zira kwallaye biyar a watanni Afrilu da Mayu.

A yanzu dai shekara guda ta rage mashi a kwangilarshi amma yanada damar sabuntata da karin shekara guda abinda yasa West Brom ke son ganawa dashi don kara maikon kwangilar.

Wakilin Odemwingie, David Omigie ya ce yanasaran za'a fara tattaunawa akan batun nan bada jimawa ba.