West Ham takai karar Sunderland akan Demba Ba

ba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Demba Ba

West Ham takai karar Sunderland zuwa mahukunta gasar Premier saboda tuntubar Demba Ba ta bayan fage.

A cewar West Ham, Sunderland ta soma tattaunawa da Ba duk da cewar kwangilarshi a Upton Park ba tare da neman izini ba.

Sunderland ta karyata zargin tuntubar dan kwallon Senegal din.

Mahukunta gasar premier sunce sun samu koke daga West Ham kuma zasu bincike lamarin.

Kakakin Sunderland yace"Kulob dinsu na sane da dokokin gasar premier akan batun cefanen 'yan kwallo".

Ba na daga cikin 'yan kwallon West Ham da ake ganin zasu bar Upton Park saboda komawar kulob daga gasar premier zuwa championship.