Fulham ta samu gurbin zuwa gasar Europa

hughes
Image caption Mark Hughes kocin Fulham

Fulham zata buga gasar Europa a kakar wasa mai zuwa sakamakon taka leda ba tare da yawan aikata laifi ba.

An baiwa Ingila gurbi guda na gasar Europa ne saboda kasancewa ta biyu wajen buga kwallo babu aikata laifuka a shekarar wasa ta 2010/11.

Chelsea itace ta samu damar amma saboda zata buga gasar zakarun Turai sai aka baiwa Fulham wacce ta zama ta biyu a bangaren.

A kakar wasa ta bana dai, sau daya tal aka baiwa tawagar 'yan kwallon Mark Hughes din.

Ana baiwa kungiyoyi maki ne bayan kowanne wasa da suka buga tare da la'akari da jan kati da katin gargadi da kulob din ya samu.