'Bana fuskantar matsin lamba'- Messi

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Lionel Messi ne zakarun kwallon duniya na bana

Dan wasan Barcelona Lionel Messi ya ce baya fuskantar mastin lamba a yayinda kungiyarshi za ta kara da Manchester United a wasan karshe a gasar zakarun Turai.

Lionel Messi mai shekarun haihuwa 23, ya ce: "Wannan wata babbar dama ce dana samu, na karawa a wasan karshe, kuma bana fuskantar mastin lamba ko kadan."

"Ina matukar son ganin ina kayatar da mutane idan ina taka leda, kuma ni da abokan wasana zamu yi duk mai yiwuwa domin mu lashe kofin."

Ya kara da cewa: "Ina yawan daukan abubuwa cikin sauki, kuma bana wani fargaba, saboda nasan yadda nasara ke zuwa garemu a 'yan kwanakin nan."