Real Madrid ta kori Valdano saboda Mourinho

valdano Hakkin mallakar hoto 1
Image caption Jose Mourinho da Jorge Valdano

Real Madrid ta kori Darekta Janar Jorge Valdano bayan gudanar da taron kwamitin mahukuntanta a filin wasa na Bernabeu.

Shugaban Real Madrid Florentino Perez yace"Mun yanke shawarar kawo karshen kwangilarmu da Jorge Valdano".

Cire Valdano na daga cikin tsarin yiwa Real garan bawul don karfafa mukamin Jose Mourinho a matsayin koci.

An samu takun saka tsakanin Valdano da Mourinho a lokacinda Mourinho ya bukaci ya sayi sabon dan kwallon gaba don maye gurbin Gonzalo Higuain a farko kakar wasa ta bana.

Perez yace "bisa abinda ya faru a kakar wasan da aka kamalla ya kamata a baiwa mai horadda 'yan wasa damar cin gashin kanshi".

A kakar wasa na farko da Mourinho ya jagoranci Real Madrid, kulob din ya lashe kofin Copa del Rey a karon farko cikin shekaru 18, bayan sun samu nasara akan Barcelona daci daya me ban haushi.