An hallaka 'yan sanda hudu a jihar Borno

Image caption 'Yan sandan Najeriya na fuskantar hare-hare a jihar Borno

Rundunar 'yan sandan jahar Borno ta ce, jami'anta wajejen hudu sun hallaka, tare da wasu fararen hula, a artabun da suka yi yau da maharan da ake jin 'yan kungiyar Boko Haram ne.

Lamarin ya faru da sanyin safiyar yau, lokacin da 'yan bindigar suka kai hari a wani caji ofis, da barikin 'yan sanda, da kuma wani banki, a garin Dambuwa mai tazarar kilomita hamsin daga birnin Maiduguri.

Sun yi ta harbe-harbe da bindiga, da kuma jefa bama-bamai.

Ko a jiya ma sai da aka yi dauki-ba-dadi tsakanin sojoji da 'yan Boko Haram din, a unguwar Mashamri, kwanar Yobe, dake cikin garin Maiduguri.