An dakatar da Kolo Toure na tsawon wata shida

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kolo Toure

Dan wasan bayan Manchester City, Kolo Toure ba zai taka leda ba a farkon wasannin kakar wasa na gaba bayan an dakatar dashi na tsawon watanni shida saboda an same shi da laifin shan haramtattun kwayoyi.

An koma da dakatarwar baya, inda zai fara ne daga ranar biyu da watan Mayu, wato ranar da kungiyarshi ta fara dakatar da shi.

Zai iya fara taka leda ne a ranar biyu ga watan Satumba, kuma za'a a rika yimai gwaji akai-akai na tsawon shekaru.

"Ina cikin mawuyacin yanayi, ban ji dadin yadda ban samu na taimakawa abokan wasa na ba, a gasar cin kofin FA da kuma gurbin da muka samu a gasar zakarun Turai." In ji Toure.

"Amma hankali na ya kwanta yanzu ganin cewa zan dawo taka leda a watan Satumba, kuma ina matukar godiya ga hukumar FA saboda irin datakun da ta nuna."

Wata hukumace mai zaman kanta ta dau matakin ladabtarwa, kan dan wasan a ranar alhamis.