Fifa ta dakatar da Hammam da Warner

Image caption Jack Warner da Bin Hammam

Hukumar dake kula da kwallon kafa a duniya Fifa ta dakatar da manyan jami'anta biyu bisa zargin cin hanci.

Kwamitin da'a na Fifa a taronshi a Zurich ya ce shugaban hukumar kwallon nahiyar Asiya Mohammed Bin Hammam da mataimakin shugaban Fifa Jack Warner suna aikata ba dai dai ba.

Mataimakin shugaban kwamitin Petrus Damaseb ya ce an dakatar dashi Mista Bin Hammam na wucin gadi daga shiga harkar kwallo a kasarshi da duniya baki daya har sai an kamalla bincike akanshi haka shima Jack Warner.

Kwamitin dai ya wanke shugaban Fifa Sepp Blatter.

Dama dai hukumar kwallon kasar Pueto Rico c, ta yi zargin cewar Mr Warner ya shirya taron da aka baiwa wakilai dala dubu 40 don su zabi Bin Hammam a zaben Fifa na ranar Laraba.

Tuni dai Mista Hamman ya janye takarar shugabanci Fifa da yake yi kafin kwamitin ta bayyana matakin da ta dauka.

A yanzu haka dai Sepp Blater ne zai tsaya takarar shugabancin hukumar, shi kadai.