Zan kara shekara guda a Barcelona-Guardiola

pep guardiola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Pep Guardiola

Pep Guardiola ya ce yanason cigaba da kasancewa kocin Barcelona bayan ya jagoranci tawagar ta lashe gasar zakarun Turai na biyu a kakar wasanni uku.

Kafin Barcelona ta lallasa Manchester United daci uku da daya a ranar Asabar a filin Wembley, akwai jitar-jitar cewar watakila wasan karshe da Guardiola zai jagoranci Barca.

Guardiola yace"ina da niyyar cigaba na karin shekara guda bayan haka sai mu gani".

A watan Fabarairu ne ya sabunta kwangilarshi a Barca zuwa karshen kakar wasa mai zuwa.

Xavi Hernandez da Andres Iniesta da Lionel Messi sune suka taimakawa Barcelona ta lashe gasar zakarun Turai a wadanan shekarun.

Guardiola ya kara da cewar"makomata zata kasance da zafi ".

Guardiola ya lashe kofin goma cikin shekaru uku a Barca bayan shafe shekaru 17 a matsayin dan wasan kulob din.

Sir Alex Ferguson wanda ya kasance manajan da yafi kowanne samun nasara a Ingila, sai dai ya shafe shekaru 25 kafin ya samu nasarorin da Guardiola ya samu a Barcelona.