'Qatar ta sayi kuri'ar gasar cin kofin duniya'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jack Warner yana ganawa da Manema labarai

Mataimakin shugaban hukumar kwallon kafa na Fifa da aka dakatar Jack Warner ya zargi Mohamed Bin Hammam da siyan kuri'un da suka baiwa Qatar damar daukar bakoncin gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022.

Warner ya ce sakatare Janar din hukumar wato Jerome Valcke ya turo masa wani sakon e-mail inda yake cewa; "Bin Hamman na nema ya sayi kujerar shugabancin Fifa kamar yadda ya sayi damar da aka baiwa Qatar."

Valcke a martaninsa ya ce; " Sakon dana turawa Warner bana kowa da kowa bane, sakon nashi ne kawai, kuma ina ganin ya wallafi shi domin ya kitsa makirci."

"Ya turo mun sakon e-mail ne yana tambayata, in tursasa Bin Hammam daga tsaya takara." In ji Valcke.

Har wa yau Valcke ya musanta zargin da ake yi na cewa yana da hannu a dakatarwar da kwamitin da'a ta yiwa Warner da Bin Hammam.